
A ranar 3 ga watan Yuni, mataimakin sakataren majalisar dokokin Cambodian kuma shugaban kwamitin masu ba da shawara ga majalisar Chheang Vannarith ya ziyarci BFSU. Shugaban jami’ar BFSU kuma mataimakin sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar Jia Wenjian ya gana da shi, inda suka cimma ra’ayi game da zurfafa mu’amala a fannin ilmi da al’adu, da yalwata haƙiƙanin haɗin gwiwa a tsakaninsu.
Bayan ganawar, Chheang Vannarith ya gabatar da jawabi, gami da yin mu’amala da ɗalibai da malamai na jami’ar.