
Daga ranar 11 zuwa ranar 14 ga watan Mayu, shugaban jami’ar BFSU kuma mataimakin sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar Jia Wenjian ya shugabanci tawaga don kai ziyara a Rasha, inda ya ziyarci jami’o’in MSLU da MSU da RUDN da RSUH da SPbSU da cibiyar nazarin gabashin duniya na kwalejin binciken Rasha, sannan kuma sun ziyarci ofishin jakadancin Sin dake ƙasar Rasha, da ƙaramin ofishin jakadancn Sin da ke birnin Saint Petersburg, da kamfanin Delo, kana sun halarci bikin buɗe abokan karatu na BFSU a Rasha.