Babban Shafi > Labaru > 正文

Yarjejeniyoyi tsakanin BFSU da jami’o’in Rasha sun zama manyan sakamakon da aka samu a taron ƙolin ƙasashen Sin da Rasha

Updated: 2026-05-26

A ranar 20 ga watan Mayu da yamma, shugaban ƙasar Sin Xi Jinping da takwaransa na ƙasar Rasha Vladimir Putin sun halarci bikin ƙaddamar da shekarun ilmin Sin da Rasha a babban taron taruwar jama’a, abin da ya shaida buɗe shekarun mu’amala a fannin ilmi tsakanin Sin da Rasha, waɗanda za a shafe shekaru 2 ana yinsa.

       Bisa goron gayyata da aka yi, shugaban jami’ar BFSU kuma mataimakin sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar Jia Wenjian ya halarci bikin. Yarjejeniyar haɗin gwiwa game da koyar da Rashanci tsakanin jami’ar BFSU da jami’ar RUDN ta Rasha da takardar fahimtar juna game da haɗin gwiwa a wajen manufofin ilmi da matasa tsakanin BFSU da hukumar kula da harkokin matasa ta Rasha sun shiga jerin takardun sakamakon haɗin gwiwa da aka samu a yayin shawarwarin shugabannin ƙasashen biyu.


Baidu
map