
A ranar 3 ga watan Yuni, ministan kula da harkokin ilmi, da kimiyya, da matasa a ƙasar Georgia Givi Mikanadze ya shugabanci tawaga don kai ziyara a BFSU, inda ya gabatar da jawabi, gami da yin mu’amala da malamai da ɗaliban jami’ar.
Jakadan Georgia a Sin Paata Kalandadze, da mataimakin ministan da kula da ilmi, da kimiyya, da matasa Levan Ghirsiashvili, da shugaban jami’ar BFSU kuma mataimakin sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar Jia Wenjian ya halarci bikin.