
A ranar 22 ga watan Mayu, mataimakin firaministan ƙasar Moldova kuma ministan harkokin wajen ƙasar Mihail Popsoi ya ziyarci BFSU. Shugaban jami’ar BFSU kuma mataimakin sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar Jia Wenjian, da zaunannen mamban kwamitin kuma mataimakin shugaban jami’ar Zhao Gang sun gana da shi.
Popsoi ya gabatar da jawabi ga malamai da ɗalibai, gami da mu’amala da su.