
Daga ranar 21 zuwa ranar 26 ga wata, shugaban jami’ar BFSU kuma mataimakin sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar Jia Wenjian ya shugabanci tawaga don kai ziyara a yankunan Hongkong da Macau da birnin Zhuhai.
A yayin ziyarar, mambobin tawaga sun halarci taron ƙoli na sha’anin koyarwa a jami’o’in Times na Asiya, inda suka ziyarci jami’ar CityU, da hukumar kula da sulhuntawa ta IOMed, da hukumar kafa dokokin Macau, da jami’ar Macau, da asusun ba da lamuni na Macau, da cibiyar nazari ta UNU Macau, da jami’ar MPU, da jami’ar MUST, da ofishin kula da tuntuɓawa na gwamnatin tsakiya a yankin musamman na Macau, da kwalejin Macau Millennium, da cibiyar ba da hidimomin ciniki a tsakanin ƙasar Sin da ƙasashen dake magana da harsunan Portugul da Spaniya, inda aka daddale yarjejeniyoyin fahimtar juna da haɗin gwiwa da yawa, kuma aka yi bincike game da shirye-shiryen tsara dokoki a yankin musamman na Macau da kafa tsarin dokoki, kana aka tattauna taron kwaikwaya M.D.D. na matasan Asiya da tekun Fasific na shekarar 2026 kuma taron tattaunawar ƙwarewar matasan duniya, sannan sun gaida abokan karatun BFSU, tare da zurfafa haƙiƙanin haɗin gwiwa a fannin raya ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa, da horar da ƙwararru, da sha’anin koyarwa da bincike, da aikin ɗab’i cikin haɗin gwiwa da mu’amala a fannin bincike.