
A ranar 20 ga watan Afrilu, shugaban jami’ar Concordia na Edmonton na ƙasar Canada Tim Loreman ya ziyarci BFSU. Shugaban jami’ar kuma mataimakin sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar Jia Wenjian ya gana da shi, inda ɓangarorin biyu suka yi shawarwari game da haɗin gwiwa a fannonin bincike a tsakaninsu.